1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Matakan kariyar cutar Ebola a Kwango

Zulaiha Abubakar
July 19, 2019

Mahukunta a Jamhuriyar Dimukuradiyyar Kwango sun umarci Sojoji tare da 'yan sandan kasar su tabbatar cewa al'ummar Goma na wanke hannaye tare da tsayawa don a binciki lafiyarsu bayan sake bullar cutar Ebola.

https://p.dw.com/p/3MIxf
Goma Ebola Untersuchung Health check
Hoto: Reuters/O. Acland

Babban jami'n wayar da kan al'umma a ma'aikatar lafiya kasar Jamhuriyar Dimukaradiyyar Kwango Dr. Aruna Abedi ya yaba wa gwamnati game da daukar wannan mataki, musamman ganin yadda wasu daga cikin mazauna garin na Goma ke bijirewa wankin hannun da gwajin lafiya. Kasashen da ke makwabaka da Kwango sun shiga fargaba biyo bayan dokar ta bacin da hukumar WHO ta ayyana a Kwango. 

Hukumar lafiya ta fara nasarar shawao an cutar Ebola kafin ta sake bullo a gabashin Kwango da wani bangare na Yuganda. Tun a ranar larabane Hukumar Lafiya ta duniya ta ayyana dokar ta baci game da Ebola da nufin daukar kwararan matakan yakar wannan cuta.