Matakan Eu na kare tekun Aden a Somaliya | Labarai | DW | 21.11.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Matakan Eu na kare tekun Aden a Somaliya

Kungiyar Gamayyar Turai ta tsawaita aikinta na kare tekun Aden na somaliya daga hare-har har i zuwa shekaru biyu masu zuwa.

Kungiyar Gamayyar Turai ta tsawaita wa'adin shirinta na yaki da fashin tekun a Somaliya i zuwa shekara ta 2016 sakamakon barazana da ake ci gaba da fuskanta daga masu fafutuka da makamai. tun dai shekara ta 2008 ne Eu ta tura da jiragen ruwa da na sama bayan da 'yan al-shabaab suka nemi gurganta jigilar kayayyaki a tekun Aden. Har yanzu dai sojojin Turai 900 da jirage birnin na sintiri da kuma jiragen ruwa na girke a wannan teku.

Dakarun na kasashen Turai sun taimaka an yi jigilar Tonne dubu 920 na abincin agaji ba tare da cin karo da #yan fashi ba a tekun na aden a cikin shekaru shidan nan da suka gabata. sai dai kuma 'yan al-Shabaab sun canja salon kamun ludayinsu inda suka fara kai farmaki da kasa tare da yin garkuwa da 'yan kasashen wajen samun kudin shiga.

Mawallafi: Mouhamadou Awal Balarabe
Edita: Abdourahamane Hassane

AFP