Matakan EU kan masu shigo da baki Turai | Labarai | DW | 23.06.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Matakan EU kan masu shigo da baki Turai

Kungiyar Gamayyar Turai EU za ta fara nuna rashin sani da dabo kan masu shigo da bakin haure ta barauniyar hanya daga Libiya.

Ministocin harkokin wajen EU sun amince da kaddamar da shirin nuna rashin sani da sabo, kan wadanda suke taimakawa bakin haure tsallaka teku domin shigowa Turai ta barauniyar hanya. A yayin taronsu da suka gudanar a kasar Luxembourg, manyan jami'an dipolomasiya suka ce za su fara ne da sa kafar wando guda da duk wadanda za su samu da hannu a harkar shigo da bakin haure a teku, sannan daga bisani su fadada shirin i zuwa kasar Libiya bayan sun samu izini daga hukumomin Tripoli.

Su dai kasashen na Turai sun yi imanin cewar wannan shirin zai bayar da damar rage mace-macen bakin haure a tekun Baharrum, tare da magance matsalar fasakwabrin mutane daga Libiya zuwa Turai ta hanyar da ba ta dace ba.

Dubban 'yan Afirka ne ke ratsa tekun Bahruum a kowace shekara domin shigowa Turai ta ko halin kaka da nufin inganta halin rayuwarsu. Sai dai kuma da dama daga cikinsu na rasa rayukansu a teku sakamakon nitsewar jiragen ruwa maras inganci da ke dauke da su.