Mataimakin shugaban Amurka ya ketare rijiya da baya | Labarai | DW | 27.02.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Mataimakin shugaban Amurka ya ketare rijiya da baya

Mataimakin shugaban kasar Amurka Dick Cheney ya bar kasar Afghanistan a yau bayan ya ketare rijiya da baya bayan a yau wani dan kunar bakin wake ya kai hari sansanin sojin da mataimakin shugaban na Amurka yake ziyara.

Cheney ya gana da shugaban kasar Afghanistan Hamid Karzai game da batun halinda ake ciki na tsaro a kasar ta Afghanistan da kuma batun karin taimako daga gwamnatin Amurka.

A yau da safen nan ne dai wani dan kunar bakin wake ya halaka kansa da wasu mutane da dama a bakin sansanin sojin da Cheney yake ziyarta.

Kakakin rundunar ta Amurka William Mitchell yace mataimakin shugaban na Amurka bai samu rauni ba saboda akwai kyakkayawar tsaro cikin sansanin.

Rundunar sojin Amurkan tace wasu yan kasashen waje 3 ne suka rasa rayukansu cikin wannan hari,amma wani dan jarida na kanfanin dillancin labaru na AFP da ya ganewa idanunsa yace an fito da gawarwakin mutane 11 cikin akwatuna da kuma ledoji daga cikin sansanin na Bagram.