Mata na koyon tukin jirgin sama a Najeriya | Zamantakewa | DW | 06.08.2019
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Zamantakewa

Mata na koyon tukin jirgin sama a Najeriya

A Najeriya sannu a hankali ana samun karuwar mata da ke shiga makarantun koyon tukin jirgin sama wanda a shekarun baya maza ne kadai ke yin shi.

Dalibai kan yi akalla awa daya ko fiye da haka suna shawagi da jirgi a sararin samaniya a kokarinsu na koyon tukin jirgin sama. Ryekeng Gidado dalibai mai shekaru 28 ta samu kanta a wannan makaranta a sakamakon daukar nauyinta da gwamnatinta ta Jihar Filato ta yi.

Kalubalen da ke sare wa matasa musamman mata gwiwa shi ne na tsadar kudin makarantar, domin mutum daya yana bukatar kusan Naira milyan takwas kafin ya kammala horansa, kudin da shugabannin kwalejin suka ce yana da sauki sosai idan aka kwatanta shi da na kasashen Turai. Sai dai a hakan ma kudin sun fi karfin aljihun ‘ya’yan talakawa. Farida Aliyu Yahaya ta ce iyayenta ne ke daukar nauyinta don taimaka mata cika burinta.

Flugzeugschulung in Nigeria (DW/Z. Umar)

Farida Aliyu Yahaya daliba mai koyon tukin jirgin sama a Najeriya

"Tun ina yarinya nake sha'awar tuka jirgin sama, kuma na gamsu cewa sauran ayyuka kowa zai iya yinsu, daga nan na sa wa zuciyata ina son yin abun da ya sha bam-bam da abin da kowa ke yi. Kuma ina tunanin jama’an gari suna ganin kamar maza kadai ne ke da ‘yancin tuka jirgin sama, amma gaskiya maganar ba haka take ba. Wannan aiki namu ba wani abu ne mai wahalar gaske ba, kawai dai ana bukatar ki sanya azama sosai.

Daliban da suka kamala kwalejin tukin jirgin sama ta Zaria kan samu aiki a kamfanonin jirage da ke jigila a Najeriya. Sukan kuma sami aiki har a kasashen ketare musamman a yankin Gabas ta Tsakiya. Sai dai kuma maza ne suka fi cimma moriyar kwalejin tun da aka kafa ta shekaru 55 da suka wuce. Amma a yanzu matashiya Chisom Juliet ma'aikaciya a wani kamfanin jirgin sama na Najeriya kuma take fadada karatunta, na son sauya wannan tarihi:

" Abu muhimmi shi ne a matsayinki na ‘ya mace ki sanya kwazo kuma kar ki yarda burin da kika sa a gaba ya sullube miki, ki yi kokari sosai wurin ganin kin kai ga gacci. Wahalar tukin jirgin sama ba ta kai yadda aka dauke ta ba. Ko yaya ne idan kika zo nan za ki san yadda za ki yi ki tsira da mutumcinki"

Flugzeugschulung in Nigeria (DW/Z. Umar)

Daliba mai koyon aikin gyaran jirgin sama a Najeriya

.

Sabbin dalibai 20 ne doka ta amince kwalejin ta dauka a bangaren tukin jirgin sama. Amma kuma akwai sauran fannoni kamar gyaren jirgi da bai wa jirgi umarni da shima akwai nasu adadin da aka kayayde musu. Amma duk da haka kwalejin ta ce tana ba mata kulawa ta musamman.

Dalibai sun yi amannar cewa tukin jirgin sama abu ne wanda kowa zai iya yi dalilin ma da ya sa kenan ba sa nuna kasala a cikin shekaru biyu da ake koyar da tukin duk da zullumin aukuwar hadarin jirgin sama a lokacin da ake koyon sanin makamar aiki.