Mata na fuskantar barazana a duniya | Labarai | DW | 08.03.2018
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Mata na fuskantar barazana a duniya

Yau ce ranar da Majilisar Dinkin Duniya ta ware domin duba irin ci gaba ko akasin haka da matan suka samu ko'ina a duniya.

Ranar wacce MDD ta yi ikirarinta tun a shekara ta 1977 na zuwa ne a dai dai  lokacin da rahotannin na kungiyoyin kare hakin dan Adam ke nuna cewar matan na fuskantar cin zarafi  da barazana a cikin kasashe da dama na duniya. Yanzu haka ko'ina a manyan birane na duniya ana gudanar da bukukuwa don ranar ta mata.