Mata na fiskantar cin zarafi a duniya | Siyasa | DW | 25.11.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Mata na fiskantar cin zarafi a duniya

Yayinda duniya ke bikin ranar cin zarafin mata ta duniya, rahotanni sun nuna cewa har yanzu mata na fiskantar matsaloli a rayawarsu, idan muka yi misali da Najeriya

Ranar 25 ga watan Nuwambar, rana ce da Majalisar Dinkin Duniya ta ware, domin yaki da cin zarafin mata, kana da yin nazari ko akasin na yaki da wannan mummunan al'ada tsakanin al'umma.

Bayanai da a Majalisar Dinkin Diniya ta fitar ya nuna cewa mata 35% na fadin duniyar na fama da cin zarafi a rayuwar su, inda ake ganin alkaluman ka iya karuwa bisa la'akkari abubuwan da ke faruwa a sassan duniya. Wannan da ma sauran dalilai ne ya sa aka ware wannan rana domin yaki da cin zarafin da ake yiwa mata musamman a kasashe masu tasowa da kuma wadan da ke fama da rikici.

Bikin wannan rana ta bana na zuwa ne a dai-dai lokacin da ake samun karuwa cin zarafin mata a Najeriya, inda ake samun karuwa yi wa yara mata fyade da kuma yadda ake ci gaba da azabtar da mata, tare da tauye musu yancin karatu. Fyade wa yara mata masu kanan shekaru ya zama rowan dare gama duniya, inda akullum ake samun rahotanni ko kuma kararraki da aka shigar na fyade a sassan Najeriya, ban da ma wanda iyaye kan boye sabo da gudun fallasa, abinda ya samu diyar don rayuwarta ta gaba.

Masu fafitikar kare hakkin mata na ganin rashin dokoki ne da kuma hukunci mai tsauri gami da halayyar wasu ma'aikata, ya sa aka kasa shawo kan wannan matsala. Yanzu haka sama da ‘yan mata 270 na hannun 'yan kungiyar Boko Haram, inda suka kwashe sama watanni shida ba tare da sanin halin da suke ciki ba, bayan kame a wata makarantar sakandare a garin Chibok dake jihar Borno.

Wannan lamari wanda ya ja hankalin kasashen duniya ya kasan ce abin tashin hankali, tsakanin iyaye da sauran masu fafitikar kare hakkin mata. Masharhanta dai na ganin ya zama dole a magance matsalar tsaron, da ake fama da shi kafi a samu saukin kame ‘yan matan da ake yawan samun, musamman a yankin Arewa maso gabashin Najeriya.

Sauti da bidiyo akan labarin