Masu zanga-zanga sun fantsama titunan Tel Aviv
July 7, 2024A Isra'ila, masu zanga-zanaga sun mamaye hanyoyin birnin Tel Aviv domin mika bukata ga gwamnatin kasar da ta cimma yarjejeniyar sakin wadanda Hamas ke tsare da su, yayin da aka shiga wata na 10 da fara yakin Gaza.
Masu boren dauke da tutoci sun haifar da cunkuso a birnin, inda suke yin kira ga gwamnati da ta gudanar da zabe.
Tun da fari dai, jami'an 'yan sanda sun tsaurara matakan tsaro a kusa da gidan Firanminista Benjamin Netanyahu da ke birnin Kudus. Ko a ranar Asabar, sai da 'yan sanda suka tarwatsa masu zanga-zangar adawa da gwamnati da suka rufe manyan hanyoyi.
A yanzu haka masu shiga tsakani a yakin na Gaza sun kaddamar da sabuwar tattaunawa a tsakanin Isra'ila da Hamas, inda 'yan uwan wadanda ake tsare da su suka bayyana kyakyawan fata a kai.