Masu tonon zinariya sun mutu a Burkina Faso | Labarai | DW | 28.08.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Masu tonon zinariya sun mutu a Burkina Faso

Mutane takwas suka mutu yayin da wasu suka samu raunuka, bayan da wani wurin da ake hakar zinariya na gargajiya ya rufta a karamar hukumar Gogo da ke tsakiyar kasar Burkina Faso.

Kinderarbeit in Goldminen in Burkina Faso (DW)

Yara masu tonon Zinare a Burkina Faso

Magajin garin wannan karamar hukuma ta Gogo, Bernard Bouda, ya sanar da wannan labari bayan ziyarar da ya kai a inda hadarin ya afku. Ana sa ran ruwan sama kamar da bakin kwarya da ke zuba a yankunan ne suka haddasa zaftarewar kasa, wanda hakan ta sanya wurin hakar ma'adinan na zinariyar ya fada wa masu aikin tonon ta. Magajin garin na Gogo ya ce bayan hukumomi su tabbatar da mutuwar mutanen, an yi musu jana'iza a garin da wannan hadarin ya afku.

Masu tonon zinariyan na Burkina Faso dai na yin wannan aiki ne duk kuwa da haramcin da hukumomi suka yi ta sabili da lokaci ne na damina inda kasa ka iya zaftarewa a kowane lokaci.