Masu rajin kare muhalli 200 ne aka kashe a 2016 | Labarai | DW | 13.07.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Masu rajin kare muhalli 200 ne aka kashe a 2016

Wani rahoto da kungiyar Global Witness mai rajin kare muhalli ta fitar a wannan Alhamis din, ya ce akalla mutane 200 masu fafutikar kare muhalli aka kashe a shekara ta 2016 a duniya

Ermordung Ashaninka Stamm Führer Tochter (Getty Images/AFP/J. Samad)

Diana Rios Rengifo 'yar wani babban dan gorgomayawa kan muhalli na kasar Honduras.

Rahoton ya zayyana sunayen kasashe inda lamarin yafi kamari. A kasar Brazil an kashe mutun 49, a Kolumbiya 37, a Philippines mutun 28, a kasar Indiya mutane 16 inda kungiyar mai zaman kanta ta ce su ne kasashen da aka fi samun kashe-kashen mutanen da ke fafutikar kariyar muhalli, adadin da kungiyar ta ce ya yi munin gaske, inda a shekara ta 2015 aka kashe mutane 185 masu fafutikar kare muhallin a duniya a wurare kamar na hakar mu'adinai, gandun daji, ko kuma cikin ruwa.

Masu fafutikar kariyar Muhalli dai a duniya na kara karuwa, sai dai kuma masu neman gurbata muhalli da ke adawa da hakan na yi musu daukan dauki dai-dai a fadin duniya, inda kungiyar ta Global Witness ta ce kashi 40 cikin 100 na mutanen an kashe su ne a yankunansu.