1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An bukaci janye dokar han zanga-zanga a Najeriya

December 10, 2020

Masu kare hakkin bil adama sun bukaci gwamnatin Tarayyar Najeriya da ta janye dokar tabacin da ta saka na hana zanga-zanga a kasar.

https://p.dw.com/p/3mXvZ
Nigeria Präsident Mohammadu Buhari
Hoto: Getty Images/AFP/P.U. Ekpei

Daidaiku da ma kungiyoyin masu kare hakin dan adam na ciki da wajen kasar, sun nemi da gwamnatin Tarayar Najeriya da ta janye dokar hana zanga-zangar da ta kakaba a kasar.

Bukatar hakan ya yi daidaitoni da ranar kare hakin bil adama ta duniya, masu kare hakin na dan adam sun mika wata budaddiyar wasika zuwa ga shugaba Muhammadu Buhari, inda suka bukaci da a saki masu zanga-zangar da ake rike dasu tare da hukunta jami'an tsaron da aka samu da hannu wajen muzgunawa al'umma.

Hukumomin kasar dai sun haramta zanga-zanga ko ma wace iri ce, tun lokacin boren adawa da cin zarafin da 'yan sanda SARS ke yi wa al'ummar kasar.