Masu gwagwarmaya na IS sun ƙwace cibiyoyin tsaro a Kobane | Labarai | DW | 10.10.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Masu gwagwarmaya na IS sun ƙwace cibiyoyin tsaro a Kobane

Ƙungiyar ta IS ita ce ke da iko da kusan kishi 40 cikin ɗari na birnin, a dai dai lokacin da Amirka ke ƙara matsa lamba ga Turkiya da ta ba da haɗin kai domin shiga yaƙin.

Rahotanin daga Siriya na cewar 'yan gwagwarmaya masu yin jihadi na Ƙungiyar IS sun ƙwace iko da babbar cibiyar tsaro ta Ƙurdawa da ke a garin Kobane da ke a arewacin Siriyar kan iyaka da Turkiya.

Masu aiko da rahotannin sun ce mayaƙan na IS sun kuma mamaye manyan gine-gine na gwamnatin yankin da wata cibiya ta mayaƙan sa kai na Ƙurdawan.