Masu fafatukan Siriya: An kashe mutane 500 a Aleppo | Labarai | DW | 10.02.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Masu fafatukan Siriya: An kashe mutane 500 a Aleppo

A ranar 1 ga watan Fabrairu gwamnati da ke samun goyon bayan jiragen saman yakin Rasha ta kaddamar da hare-hare kan lardin na Aleppo.

Alkaluman da masu fafatuka na kasar Siriya suka bayar na nuni da cewa sama da mutane 500 aka kashe tun lokacin da sojojin gwamnati suka fara farmaki a lardin Aleppo. Kungiyar lura da hakin dan Adam a Siriya ta ce daga cikin wadanda aka kashe akwai 'yan tawayen Siriya da masu ikirarin jihadi na ketare 274 sai kuma fararen hula 89 ciki har da yara 23. A ranar 1 ga watan nan na Fabrairu gwamnati da ke samun goyon bayan jiragen saman yakin Rasha ta kaddamar da hare hare kan lardin na Aleppo, abin da kuma ya tilasta tserewar dubban mutane zuwa kan iyaka da kasar Turkiyya. Babu wata kafa mai zaman kanta da ta tabbatar da alkaluman da kungiyar mai mazauni a birnin Londin kuma ke da alaka da 'yan tawayen Siriya ta bayar.

A dangane da rikicin na Siriya ministocin tsaro na kasashen kungiyar NATO sun fara wani taro a birnin Brussels bisa shawarar da kasashen Jamus da Turkiyya suka bayar cewa ya kamata kungiyar NATO ta shiga aikin sa ido a gabar tekun Turkiyya a kokarin magance matsalar 'yan gudun hijira da ke gujewa daga yakin na Siriya.