Masu cutar HIV na neman agajin gaggawa | Zamantakewa | DW | 25.04.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Zamantakewa

Masu cutar HIV na neman agajin gaggawa

Sama da mutane miliyan uku da ke dauke da kwayoyin wannan cuta da ke karya garkuwar jikin dan Adam a Najeriya kuma mutane 900,000 ne kawai ke samun damar shan magani na kashe kaifin cutar.

Hukumar yaki da cuta mai karya garkuwar jiki ta HIVAIDS wato NACA a Najeriya ta nunar cewar da daman masu  dauke da cutar yanzu basa iya samun magani a dalili na karancin tallafi da aka saba samu daga cibiyoyin Duniya daban daban, sannan kuma gwamnatin Najeriya bata hobbasar da ta kamata kan yaki da cutar.

Da daman dai yanzu masu dauke da cutar na kokawa ,ganin ma cewar yanayin da aka shiga din na jallin mutuwar da damansu.

Flash-Galerie AIDS Projekte (AP)

Sama da mutane miliyan uku da ke dauke da kwayoyin wannan cuta da ke karya garkuwar jikin dan Adam a Najeriya kuma mutane 900,000 ne kawai ke samun damar shan magani na kashe kaifin cutar a Najeriya, wannan kuwa na zuwa ne saboda kasancewar da dama tallafi da ake samu na kungiyoyi na kasashen duniya wadanda ke bada tallafi mafi girma a aikin tallafin. Gwamantin Najeriya dai na bada kashi 20 cikin dari ne kawai ta ke bayarwa adadin da ba ya isa. Wata mata a jihar Rivers Kudu maso Kudancin Najeriya ta ce babban kalubale da ke gabansu shi ne yadda za su samu maganin da ke kashe kaifin cutar ko kuwa su kasance cikin barazanar karewa.

Jihar ta Rivers dai ta kasance cikin goma na wadanda cutar ta fi kamari a kasar ta Najeriya, wannan ya sanya masu fafutikar tallafa wa masu cutar HIV ke kira na gwamnati ta kai musu agaji cikin gaggawa, kasancewar a jihar ta Rivers ma kananan hukumomi uku ne kawai ke tallafawa mutanen cikin  23 na jihar.

NACA dai ta ce za ta ci gaba da jan hankalin kungiyoyi da ke tallafawa a wannan yaki da cutar ta HIV mai halaka jama'a.