1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Masu bincike na Faransa za su tantance tarkacen jirgin sama

Suleiman BabayoAugust 1, 2015

An kai abin da ake tsammani tarkacen jirgin saman nan ne na Malesiya da ya bace zuwa kasar Faransa daga inda aka samu a tsibirin Reunion.

https://p.dw.com/p/1G8GU
Wrackteil Malaysia Airlines Flug MH370
Hoto: picture-alliance/dpa/Zinfos974

Rahotanni daga birnin Paris na kasar Faransa sun tabbatar da cewa jirgin saman dauke da wani abin da ake tsammani tarkacen jirgin saman Malesiya da ya bace fiye da shekara guda da ta gabata, ya sauka inda za a gudanar da bincike. An samu wannan sashi na jirgin sama a tsibirin Reunion na tekun Indiya da ke karkashin ikon kasar Faransa.

Idan masu bincike a birnin Toulouse na kudu maso yammacin Faransa suka tabbatar abin da aka samu wani bangare ne na jirgin saman kasar Malesiya da ya bace watanni 16 da suka gabata, haka ya zama alama ta farko na kai wa ga gano abin da ya samu jirgin saman kiran Boeing 777 mai lamba MH370 wanda ya tashi daga Kuala Lumpur babban birnin kasar Malesiya a kan hanyar zuwa birnin Beijing na kasar China dauke da mutane 239.

Tuni mahukuntan Malesiya suka nuna tabbacin cewa abin da aka samu ya kasance bangare na jirgin saman da ya bace tun watan Maris na shekara ta 2014.