Masu aikin agaji na cigaba da gano gawawwaki a Bangladesh | Labarai | DW | 24.04.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Masu aikin agaji na cigaba da gano gawawwaki a Bangladesh

Duk da cewa ba'a kai ga tantance yawan waɗanda suka hallaka ba, ana kyautata zaton fiye da mutane 700 suka yi rauni

Masu aikin kwana-kwana a Bangladesh na cigaba da gano gawawwakin waɗanda suka rasu bayan da wani gini mai hawa takwas ya afka musu, kawo yanzu dai ma'aikatan sun ce sun gano gawawwaki 123 waɗanda ɓarɓuzan gini suka danne, kuma da yawa na nan a maƙale a ginin da ke wajen Dhaka bisa bayyanan 'yan sanda.

Yawancin wadanda suka rasu mata ne waɗanda suke aiki a masaƙu hudun da ke ginin.

Kawo yanzu dai ba'a kai ga tantance yawan mutanen da ke aiki a lokacin da hatsarin ya faru ba sai dai hotunan talibijin sun nuna ɗaruruwan 'yan uwa da abokan arziƙi a kusa da ginin suna juyayi, suna riƙe da hotunan 'yan uwansu da ke aiki wurin domin nunawa masu aikin ceton.

Mawallafiya: Pinaɗo Abdu Waba
Edita: Umaru Aliyu