Maslaha game da yakin basasar Siriya | Labarai | DW | 11.11.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Maslaha game da yakin basasar Siriya

A yanzu 'yan adawar Siriya sun bayyana kudirin halartar taron sulhu na Geneva.

'Yan adawar kasar Siriya da ke samun goyon bayan kasashen yammacin duniya sun sanar da cewar, za su halarci taron kasa da kasa domin samar da mafita ga rikicin kasarsu, wanda birnin Geneva zai kaibi bakunci. Wannan labarin na kunshe ne cikin wata sanarwar da hadaddiyar kungiyar 'yan adawar kasar ta Siriya ta fitar da safiyar wannan Litinin (11. 11. 13). Sai dai kuma 'yan adawar sun bada sharadin cewar, tilas ne a samar da wata gwamnatin wucin gadin da za ta mayar da Siriya bisa turbar dimokradiyya a matsayin hanyar kawo karshen yakin basasar kasar na tsaawon kimanin shekaru biyu da rabi kenan.

Hakanan sun gindaya sharadin bayar da dama ga hukumomin bayar da agaji kai wa ga yankunan da ake yi wa kawanya, da kuma sakin fursunonin siyasa, game da cewar, tilas ne duk wani babban taron da ya shafi siyasa ya kasance yana da manufar tsara hanyar komawa kan tafarkin siyasa a kasar. Sai dai kuma akwai wani bangare na 'yan tawayen da yayi watsi da halartar taron na Geneva, muddin dai ba zai kai ga cire shugaba Assad daga mulki ba, kana akwai ma wasu 'yan tawayen da suka ce za su dauki duk wanda ya halarci taron a matsayin wanda ya ci amanar kasar.

Mawallafi : Saleh Umar Saleh
Edita : Umaru Aliyu