Maslaha ga rikicin kudin Girka | Labarai | DW | 04.07.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Maslaha ga rikicin kudin Girka

Jamus ta yi marhabin da abin da ta kira labari mai dadin daga Girka.

Ministan kula a harkokin wajen Jamus Guido Westerwelle, ya jaddada gamsuwarsa game da ingancin matakan farfado da tattalin arzikin kasar Girka, wadda ta fada cikin matsalar koma bayan tattalin arziki, inda ya ce a karshe an fara samun labari mai dadi game da hakan. Westerwelle, wanda ya gana da firaministan kasar ta Girka, Antonis Samaras, yayin wata ziyarar da ya kai, ya fadi, bayan ganawar cewar, dama ya je kasar ne dauke da sakon fatan alheri, dubi da da irin ci gaban da take samu bayan daukar matakan tallafa mata, yana mai cewar, Jamus na nuna goyon baya da kuma girmamawa ga kasar ta Girka. Dama dai Girka ta fada cikin rikicin kudin da ya tilasta wa hukumomin kasar aiwatar da shirin tsuke bakin aljihun da ya janyo bore, da kuma yaje-yajen aiki a sassa daban-daban na kasar.

Mawallafi : Saleh Umar Saleh

Edita : Umaru Aliyu