1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Masar tana ɗaukan mataki kan Libiya

Suleiman BabayoFebruary 16, 2015

Gwamnatin Masar ta ce za ta ci gaba da ɗaukan mataki kan mayaƙan da ke Libiya

https://p.dw.com/p/1Ecc8
Ägypten Reaktion auf Ermordung koptischer Christen durch IS
Hoto: imago/Xinhua

Shugaba Abdel Fattah al-Sisi na ƙasar Masar ya yi alƙawarin ci gaba da ɗaukan mataki kan mayaƙan ƙungiyar neman kafa daular Musulunci na ƙasar Libiya da suka hallaka 'yan Masar 21. Yayin da jiragen saman yakin ƙasar suka kai farmaki kan maboyar mayakan.

Ƙasar Hadaddiyar Daular Laraba ta bai wa kasar Masar goyon baya bisa hare-haren da ta ƙaddamar kan ƙungiyar neman kafa daular Islama ta kasar Libiya, bayan mayaƙan ƙungiyar sun hallaka 'yan kasar ta Masar 21 Kiristoci mabiya ɗarikar Coptik.

A wannan Litinin rahotanni sun nuna cewar jiragen saman yaƙin ƙasar ta Masar sun ci gaba da luguden wuta kan wuraren da ake zargin mayaƙan da suka hallaka 'yan Masar suna buya. Shugaban Kiristoci mabiya ɗarikar Katolika na duniya Papa-Roma Francis ya nuna bakin-ciki da kisan da aka yi wa 'yan ƙasar ta Masar. Tuni mahukuntan Masar suka nemi ƙawancen da Amirka ke jagoranta da suka kai farmaki kan mayakan IS na Libiya.