1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Masar tana ci gaba da fuskantar rikicin siyasa

July 16, 2013

Fiye da mutane 20 sun samu raunika yayin fito-na-fito tsakanin jami'an tsaron Masar da masu zanga-zanga.

https://p.dw.com/p/198AM
Hoto: Reuters

Jami'an tsaron kasar Masar sun yi fito-na-fito da magoya bayan hambararren shugaba Mohammed Mursi tun cikin daren wannan Litinin (15.07.13) zuwa sanyin safiyar wannan Talata (17.07.13).

Tashin hankalin ya samo asali ne lokacin da masu zanga-zangar suka yi yunkurin toshe babbar gadar kogin Nilu. Masu zanga-zangar sun yi amfani da duwatsu wajen jifar 'yan sanda, wadanda suka mayar da martani ta hanyar watsa hayaki mai-saka hawaye, akwai kimanin mutane 22 da suka samu raunuka.

'Yan kungiyar 'yan Uwa Musulmai sun nemi janar Abdel Fattah al-Sisi wanda ya jagoranci juyin mulki ya yi murabus daga aikin soja, sannan a mayar da Mursi kan madafun iko. Duk wannan lamarin na faru wa ne yayin da mataimakin sakataren harkokin wajen Amirka William Burns ya gana da sabbin mahukuntan kasar ta Masar.

Mawallafi: Suleiman Babayo
Edita: Saleh Umar Saleh