Masar ta tsawaita wa′adin al-Sisi | Labarai | DW | 17.04.2019
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Masar ta tsawaita wa'adin al-Sisi

Majalisar dokoki a Masar, ta yi wa kundin tsarin mulkin kasar gyaran fuska, ta yadda zai bai wa Shugaba Abdel Fattah al-Sisi damar ci gaba da mulki har zuwa shekara ta 2030.

Majalisar mai wakilai 596 wadanda galibi ke goyon bayan Shugaba al-Sisi, ta amince da gagarumin rinjaye ne cikin watan Fabrairu kafin ta tabbatar da gyaran a ranar Talata.

Sai dai za a kada kuri'ar ra'ayin 'yan kasa a farkon watan Ramadanan bana, da ke iya kamawa a ranar biyar ga watan gobe na Mayu.

Idan kuma aka kammala kuri'ar ta raba gardama, shugabannin kasa a Masar za su rika yin shekaru shida ne sau biyu.

Hakan kuwa na nufin za a yi wa shugaba mai Abdel Fattah El-Sissi wanda ke wa'adinsa na biyu, karin wasu shekaru biyu na mulkin da yake kai.

Kazalika, zai sake takara a shekara ta 2024.