1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Mahukuntan Masar sun saki dan Jarida

Zulaiha Abubakar
March 4, 2019

Mahukuntan kasar Masar sun saki wani dan jarida da ya shafe sama da shekaru biyar a tsare bayan samun sa da daukar hoton yadda sojojin kasar suka kashe daruruwan masu zanga-zanaga a shekarar 2013.

https://p.dw.com/p/3EPdW
Mahmoud Abu Zeid
Hoto: picture-alliance/dpa/M. El-Raai

Mahmoud Abu Zeid wanda aka fi sani da Shawkan ya bayyana cewar ba zai iya kwatanta farin cikin da yake ciki ba jim kadan bayan sallamar sa daga gidan kurkuku a wannan Litinin din, ya kuma ci alwashin cigaba da aikin yada labarai duk da hadarin da 'yan jarida ke fuskanta na kisa ko cin zarafi a lokutan da suke gudanar da aiki. Kafin wannan lokaci dai Majalisar Dinkin Duniya da kungiyoyin kare hakkin 'yan Adam sun yi ta kiraye-kirayen Masar ta gaggauta sako dan Jaridar .

Gwamnatin kasar karkashin jagoranci Abdel Fattah al-Sisi na cigaba da zargin wasu daga cikin masu zanga-zangar da daukar makamai da suka yi sanadiyyar rasuwar jami'an tsaro takwas a shekara ta 2013