1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shugaban kasar Masar na ziyarar aiki a Jamus

Zulaiha Abubakar
October 29, 2018

Shugaba Abdel Fatah al-Sissi wanda ke ziyarar aiki a Jamus ya gana da shugaban kasar Frank-Walter Steinmeier da kuma kakakin majalisar Dokokin Kasar Wolfgang Schaeuble a wannan Litinin.

https://p.dw.com/p/37LwL
Deutschland - Ägyptischer Präsident Abdel Fattah al-Sisi in Berlin
Hoto: picture-alliance/dpa/W. Kumm

Yayin ganawar, shugaban kasar Jamus ya yaba da irin kokarin da gwamnatin Masar ke yi na magance aiyukan ta'addanci da kuma hana kwararar 'yan cirani zuwa kasashen Turai, a nasa bangaren Shugaba Sisi ya nemi hadin kan kasar Jamus a yunkurin da ya ke na ganin ya bunkasa tattalin arzikin Masar.