Masar ta kori jakadan Turkiyya da ke kasar | Labarai | DW | 23.11.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Masar ta kori jakadan Turkiyya da ke kasar

Kasar Masar ta bada sanarwar korar jakadan Turkiyya da ke kasar Huseyin Avni Botsali bayan da ta ce fira ministan Turkiyya ya yi kalamai marasa dadi ga gwamnatin Masar.

Turkish Ambassador in Cairo Huseyin Avni Botsali, who was called to hold a consultation on recent developments in Egypt, arrived in Ankara. Evrim Aydin / Anadolu Agency

Jakadan Turkiyya a Masar da aka kora

A ranar Alhamis din da ta gabata ce fira ministan na Turkiyya Recep Tayyip Erdogan ya yi Allah wadai da mahukuntan Masar din saboda amfani da karfi da ya ce jami'an tsaron kasar sun yi kan masu zanga-zanga da ke nuna goyon bayansu ga hambararren shugaban kasar Muhammad Mursi ranar sha 14 ga watan Agustan da ya gabata.

Mai magana da yawun ma'aikatar harkokin wajen Masar din Badr Abdelatty ya ce Alkahira ta yanke shawarar korar jakadan na Turkiyya a Masar da ma janye huldar jakadanci da ita sannan kuma ba za tura jakadanta Turkiyyan ba saboda kalaman na Erdogan katsalandan ne a harkokin cikin gidan Masar din.

Dama dai dangantaka tsakanin Ankara da Alkahira ta yi tsami tun bayan da aka hambarar da Mursi wadda a lokacin da ya ke gadon mulki jam'iyyarsa ta 'yan uwa Musulmi ke dasawa da jam'iyyar AKP ta fira minista Erdogan.

Mawallafi: Ahmed Salisu
Edita: Pinado Abdu