1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Masar ta ce ba hannunta wajen kai hari a Libiya

August 26, 2014

Abdel Fattah al-Sisi ya bayyana cewa kasarsa na tallafa wa Libiya ne ta hanyar kayan da suka jibinci ba da horon soji, ba kai mata hari ba.

https://p.dw.com/p/1D1YN
Abdel Fattah al-Sisi
Hoto: picture-alliance/dpa

Tun bayan da jami'an Amirka suka bayyana cewa jiragen yaki mallakar daular larabawa ta UAE sun yi amfani da wani sansani a Masar wajen kai hare-hare a Libya, mahukuntan birnin na Alkahira sun yi fatali da wannan zargi.

Sameh Shoukri ministan harkokin wajen ya fada wa 'yan jarida cewa Masar ba ta da wata dangantaka ta kai tsaye da wasu ayyukan soji a Libiya, sai dai su kan tallafa wa Libiya ne da bada kayan da suke bukata wajen bada horon soji.

Tuni dai shugaba Abdel Fattah al-Sisi na Masar ya bayyana cewa kasarsa ba ta da hannu kan wasu hare-hare da ake yi a Libiyan, amma Jamian Amirka sun tabbatar da cewa, a ranar Litinin jiragen yakin na daular larabawa ta UAE sun kai wasu hare-hare har sau biyu cikin kwanaki 7 ta hanyar amfani da wasu sansanoni a Masar.

Mawallafi: Yusuf Bala
Edita: Abdourrahamane Hassane