1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Za a warware takaddamar madatsar Nilu

Abdul-raheem Hassan
October 24, 2019

Shugabannin kasashen Masar da Habasha sun amince da farfado da batun madatsar ruwan Nilu da kasashen biyu ke takkadama a kai.

https://p.dw.com/p/3RtOg
Ägypten Blick auf den Nil in Kairo
Hoto: picture-alliance/ZB/M. Toedt

Yayin wani taro da shugabannin Afirka da Shugaban Rasha a birnin Sochi, Shugaba Abdel-Fattah al-Sissi na Masar da Firaiministan Habasha Abiy Ahmed sun ce nan ba da jimawa kwamitin da ke aiki kan takaddamar madatsar ruwan zai koma bakin aiki domin cimma matakin karshe kan yadda za a yi amfani da madatsar ruwan.

An dai sha kai ruwa rana tsakanin Masar da Habasha kan wannan madatsar ruwa dukkannin bangorori kowa na son iko da shi, sai dai gwamnatin Alkahira ta fi nuna damuwa ganin yadda harkokin nomanta da sauran masana'antu suka dogara kan kogin na Nilu. Yayin da Habasha ke nuna zarra kan kudi sama da dala biliyan hudu domin gina madatsar ruwan saboda samar da makamashin wutar lantarki.