1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Masanan kimiya sun samu lambar yabo ta Nobel

Yusuf Bala Nayaya
October 1, 2018

Kwararrun kimiyar kula da lafiya James Allison dan Amirka da Tasuku Honjo dan kasar Japan sun yi nasara ta samun lambar yabo ta Nobel a wannan shekara ta 2018 a fannin likitanci na Physiology ko Medicine a Turance.

https://p.dw.com/p/35ncI
Nobelpreis für Medizin 2018 Tasuku Honjo James Allison
Hoto: AFP/Getty Images/J. Nackstrand

Wannan karramawar da zakakuran masanan suka samu a wannan Litinin na zuwa ne bayan wani gagarumin aiki da suka gudanar a duniyar kimiya inda suka gano dabarun masanan kimiya wajen amfani da garkuwar jikin dan adam wajen yaki da cutar daji ko kansa a Turance. Masanan kimiyar dai sun yi aikin nasu ne a shekarun 1990 wanda ya taimaka wajen samun sauyi da amfani da sabbin dabaru wajen kula da marasa lafiya da suka harbu da cutar daji a hunhu ko a fatarsu.