Masana sun dukufa ga neman maganin Ebola | Labarai | DW | 04.09.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Masana sun dukufa ga neman maganin Ebola

A wani mataki na neman kawo karshen cutar Ebola dake lakume rayukan al'umma da dama a yammacin Afirka, masana sun dukufa wajan samar da magani mai inganci.

Rahotanni daga birnin London na kasar Birtaniya na cewa, gwajin sabon maganin nan na cutar Ebola da ma'aikatar binciken magungunna ta Johnson & Johnson ta samar, zai fara ne a farkon shekara ta 2015, abun dake nunin cewa masu bincike sun dukufa sosai na ganin sun samu gano maganin wannan mugunyar cuta mai saurin kisa.

Wasu magungunnan kuma sun kasance cikin gwajin a halin yanzu, inda daga nasu bengare GlaxoSmithKline, za su kaddamar da nasu gwajin sabon maganin a wannan watan, yayin da a hannu daya kuma wani maganin da masana masu bincike na gwamnatin kasar Canada ke aiki a kansa, za'ayi gwajin sa nan da dan lokaci kalilan. Shi dai gurin da ma'aikatar binciken ta Johnson & Johnson ta sama gaba, shine na samar da magani mai inganci bisa kasuwanni, wanda zai murkushe cuta ta Ebola da kawo yanzu tayi sanadiyar mutuwar mutane fiye da 1900 a yammacin Afirka a cewar hukumar lafiya ta duniya, WHO.

Mawallafi: Salissou Boukari
Edita : Umaru Aliyu