1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Martanin 'yan siyasa ga jawabin shugaba Ramaphosa

Abdullahi Tanko Bala
February 17, 2018

'Yan siyasa a Afirka ta kudu na ci gaba da martani ga jawabin sabon shugaban kasar Cyril Ramaphosa wanda ya bukaci jama'a su manta da abin da ya wuce a baya yana mai cewa a yanzu an shiga sabon babi na aiki tukuru.

https://p.dw.com/p/2srhL
Südafrika - neuer Präsident Cyril Ramaphosa
Hoto: Getty Images/AFP/M. Hutchings

Jawabin wanda sabon shugaban kasar ya gabatar a gaban majalisar dokoki, ya baiwa yan kasar da jami'an gwamnati kyakkyawar fata da karfafa gwiwa na makoma mai kyau a gaba tare da jaddada bukatar hadin kai ga dukkan yan kasa.

"Ya kamata mu manta da karni na rashin yarda da shakku akan hukumomi da jami'an gwamnati. Ya kamata mu manta da dukkan wasu abubuwa na rashin dadi da suka mayar da kasar mu baya saboda a yanzu sabon babi ya tunkaro mu" 

Cyril Ramaphosa ya kuma zayyana wasu muhimman kudirori da gwamnatinsa za ta aiwatar wadanda suka hada da yaki da cin hanci da rashawa da samar da abubuwan more rayuwa da kuma samar da ayyukan yi.

Südafrika - neuer Präsident Cyril Ramaphosa - Vereidigung
Majalisar dokokin Afirka ta kudu lokacin rantsar da sabon shugaba Cyril RamaphosaHoto: Getty Images/AFP/M. Hutchings

Wannan jawabi dai ya sami martani daga jami'an gwamnati da yan siyasa da kuma jama'ar gari.
Naledi Pandor ministar kimiyya da fasaha ta Afirka ta kudun ta yi tsokaci tana mai cewar.

"Muhimmin al'amari shine niyyar gwamnati ta habaka tattalin arziki mai karfi da kuma aiki tare da abokan huldarmu kamar kasar Jamhuriyar China domin tabbatar da cewa mun samar da masana'antu da samar da guraben ayyuka ga matasa don cigaban tattalin arzikin Afirka ta Kudu da al'ummarta baki daya"

Wannan ne dai karon farko cikin shekaru da dama da shugaban kasa ya gabatar da jawabi ga al'ummar kasa a gaban majalisar dokoki cikin kwanciyar hankali ba tare da hargowa daga jam'Iyyun adawa ba. Shugaban jam'iyyar Freedom party Dr Mangosuthu Buthelezi ya yi martani yana mai cewa.

"Jawabin ya nuna kyakkyawar niyyarsa, ina gani wannan ya wuce duk yadda ake zato. Jawabi ne da ya taba kowa."
To sai dai a nasa bangaren shugaban Jam'iyyar Demokratik Allaince Mmusi Maimane yace kwaryar sama ce take dukan ta kasa.

Südafrika - neuer Präsident Cyril Ramaphosa - Vereidigung
Hoto: Reuters/M. Hutchings

"Mun yi maraba da jawabin , to amma inda gizo ke sakar shine bai samar da wata mafita ta gaggawa ba. Ya dai nuna alkawarin daukar managartan matakai, amma idan ka duba babu abin da ya banbanta shi da jawabai na gwamnatin da ta shude. Muna ganin ta fuskoki da dama zai ci gaba da tsare tsaren gwamnatin Zuma."

Wani batu da ya dauki hankalin yan adawa shine na yaki da cin hanci da kuma yadda shugaban zai tunkari jami'an dake cikin gwamnati a yanzu kamar yadda shugaban jam'iyyar fafutukar tattalin arziki Julius Malema ya nunar.

"Dole ne ya kama takwarorinsa saboda suna cin hanci kuma yawancinsu ba za su ji dadinsa idan ya fara tuhumarsu"

Sabon shugaban dai Cyril Ramaphosa ya godewa tsohon shugaban kasar Jacob Zuma game da yadda ya tafiyar da batu mawuyaci kuma mai sarkakakiya na yi masa kiranye. Ya kuma gode masa bisa gudunmawar da ya bayar ga kasa.