Martanin Rahsa kan sabbin takunkumi | Labarai | DW | 04.08.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Martanin Rahsa kan sabbin takunkumi

Gwamnatin Rasha ta ce shirye ta ke da ta maida martani kan takunkumin da wasu kasashen Turai da ba sa cikin kungiyar EU ke shirin kakaba mata.

Firaministan Rashan Dmitry Medvedev ya ce tuni gwamnati ta umarci jami'anta da ta su shirya maida martani da zarar kasashen sun bi sahun EU wajen sanya musu takunkumi na karya tattalin arziki.

Ya zuwa yanzu dai mahukuntan na Rasha ba su fito fili sun ambaci sunaye wadannan kasashe da ke shirin sanya musu takunkumi ba amma sun ce shiye su ke su maida martani.

A baya EU da Amirka sun sanyawa Rashan takunkumi saboda matsayin da suka ce ta dauka kan rikicin Ukraine da ma maida yankin nan na Kirimiya karkashinta.