Martanin kungiyoyin rajin neman ceto ′yan matan da suka bata | Siyasa | DW | 22.03.2018
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Martanin kungiyoyin rajin neman ceto 'yan matan da suka bata

Kungiyar Bring Back Our Girls ta maida murtani a game da sako ‘yan matan da Dapchi da aka sace tsawon wata guda, to sai dai sun kara jaddada tambayoyi na yadda lamarin ya faru da ke jefa tababa a daukacin wannan batu.

Murna da doki da farin ciki ne ya cika fuskoki mafi yawan masu fafutukar kungiyar da ke rajin ganin an sako ‘yan matan da suka fara wannan tun daga na Chibok ya zuwa na Dapchi, wadanda a makon day a gabata suka baiwa gwamnatin wa'adi na kwanaki bakwai ta amsa masu tambayoyi guda 14 a kan yadda aka  sace ‘yan matan.

To sai dai murna ta kasance wadda ke cike da mamaki a kan yadda aka bayyana ‘ya'yan kungiyar ta Jama'atu Ahlu Sunnah Li Dawatti Wal jihad sun mayar da ‘yan matan kamar yadda suka kwashe su.

Tuni dai kungiyoyin farar hula da masu rajin kyautata al'ammura suka fara nuna ‘yar yatsa a kan yadda daukacin al'amarin ya guda  da suka ce dole ne a nemi bayani daga gwamnatin tare da yin taka tsan-tsan. Comrade Isah Tijjani mai sharhi ne kuma shugaban kungiyar kyautata al'amura ga ‘yan Najeriya day a bayyana tsoron illar da wannan ka iya yi.

A yayin da rahotanni ke bayyana sakon ‘yan matan na Dapchi da iyayensu ke cikin murna da ma  sauran ‘yan Najeriya, ga Mr Hosea Tsambido na kungiyar Chibok mazauna Abuja ya ce batun makomar ‘yan matan Chibok muhimmi ne a dai dai lokacin da ake murna da sako na Dapchi.

Zargin jefa batu na siyasa a cikin daukacin lamari ke ci gaba da daukan hankali za'a sa ido don ji da ma ganin ko za'a ladabta wasu da ake zargi da sakaci a daukacin al'amarin da ke daukan hankalin a cikin Najeriya da ma kasashen ketare.

 

Sauti da bidiyo akan labarin