Martanin gwamnatin Najeriya bisa hatsarin jirgin sama | Siyasa | DW | 20.12.2012
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Martanin gwamnatin Najeriya bisa hatsarin jirgin sama

Majalisar zartaswan Najeriya ta ƙaddamar da bincike, kan hatsarin da ya kai ga mutuwar Yakowa da Azazi

A yayin da ake ci gaba da fuskantar kace nace game da hatsarin da ya yi asarar gwamnan jihar Kaduna da kuma tsohon mashawarcin tsaron Tarrayar Najeriya, gwamnatin kasar ta kamala taron ta na shekara shekara tare da mai da hankali wajen ta'aziyar jami'an biyu.

Duk da cewar dai sun faro a cikin farin ciki da fatan sauyi ga kasar ta Najeriya sun kare ta cikin bakin ciki da alhini ga yayan majalisar zartarwar Tarrayar Najeriya da suka gudanar da wani zama na musamman domin juyayin tsohon gwamnan jihar Kaduna da sauran abokan takun da suka rasu a cikin hatsarin jirgin saman kasar na karshen mako.

Kama daga shugaba Jonathan da ya ce babu kamar su ya zuwa ragowar mataimakin sa kuma tsohon ubangida ga gwamna Yakowa dai daukacin ministocin gwamnatin kasar sun dai dauki tsawon sa'o'i suna yabo da koda mamatan biyu da suka taba zama yaya ga majalisar a lokutan baya.

Wannan ne dai karo na farko da wasu jami'an gwamnatin kasar mafi girma kan rasa rai a cikin hatsarin da sannu a hankali ke zaman ruwan dare ga kasar ta Najeriya da kuma a ke ta'allakawa da gazawar gwamantin na daukar mataki.

Tuni dai gwamnonin kasar suka ce sun ji sun gani kuma za ta kai ga sauyawa bayan gazawar mahukuntan na Abuja na fidda rahotannin jerin hatsuran kasar na baya ga jama'a balle daukar mataki bayan faruwar sa.

Flugzeugzusammenstoß in Hessen mit mehreren Toten

Yawaitar haduran jiragen sama a Najeriya

To sai dai kuma a cewar Mr Labaran Maku dake zaman ministan yada labaran kasar ta Najeriya kuma kakakin gwamnati abun da yan kasar ke bukata a yanzu haka na zaman karin hakuri da jan kafa na gwamnatin. Inda yace kamata ya yi a dauki kaddara bisa abun da Allah ya yi.

Wannan ne dai hatsari kusan na bakwai cikin tsawon kasa da shekaru biyu ga masana'antar sufurin jiragen saman kasar da ta sha tabbacin an sauya, amma kuma tasha baiwa yan kasar mamaki dama tada hankalin yan bokon dake zaman fasinjan jirgin saman kasar ta Najeriya.

Tuni dai batun shiga cikin binciken a bangaren gwamnonin kasar dama majalisun Tarayyar ta biyu ya fara tada hankulan fadar da a cewarta na zaman kokari na haifar da sabon rudani a cikin kasar. kamar yadda minstan yada labaran kasar Labaran Maku ya bayyana.

Ana dai anbaton cin hanci da rashawa a cikin sufurin jiragen saman Najeriya, amma ce an kai ga rahotannin dake ambaton sunaye, to sai dai kuma uwa a gindin murhu ta gaza kaiwa ga hukunta ko da dan bera a cikin badakalar da sannu a hankali ke zaman tsumangiyar kan hanya fyadi yaro fyadi babba.

To sai dai kuma a cewar Makun hatsarin saman ba kaya ne na kasar ta Najeriya kadai ba. Abun jira a gani dai na zaman tasirin kokarin kwantar da hankulan yan kasar ga gwamnatin da ake zargi da gazawa.

Mawallafi: Ubale Musa
Edita: Usman Shehu Usman

Sauti da bidiyo akan labarin