Martanin Ghana kan batun tsofin ′yan kason Gwantanamo | Siyasa | DW | 13.01.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Martanin Ghana kan batun tsofin 'yan kason Gwantanamo

Shugaban kasar Ghana John Dramani Mahama ya gana da yan jarida inda ya tattauna kan batun shigo da wasu tsofin 'yan fursuna ta Guantamo da kasar Amirka ta turo zuwa Ghana.

Kamar dai yadda jama’a ke ta nuna shakkunsu a gameda karban wasu fursunan Guantanamo bay guda biyu, wadanda za’a baiwa mafaka a kasar Ghana tsawon shekaru biyu. Sai dai a wata ganawa da shugaban kasar ya yi tare da manema labarai, ya bayyana cewar, babu wata fargaba acikin wannan matakin da gwamnati ta dauka.

"A matsayin kasar mu ta kungiyar kawancen Tarayyar ECOWAS, muna cikin wadanda ko wane dan kasa daga cikin wadan nan kasashe za su iya shigo wa kasar mu. Kenan ko da kuwa ana can ana yaki da kungiyar Boko Haram ai wannan damar ta ECOWAS ta ba su yancin shiga acikin kowane dayan kasashen ECOWAS ba tareda visa ba, a dalilin haka abu mahimmi a irin wannan hali shi ne samun cikakkun bayanan wadanda ke shigowa kasar saboda nasabar su da ayyukan ta’addanci."

Sai dai kuma shugaban ya kara da bayyana irin alfanon da kasar Ghana za ta iya samu a sakamakon bada wannan damar ga kasar Amirka.

"kasashen da suka yi fice wajan samun bayanan wadanda ake zargi da ayyukan ta’addanci su ne Amirka, Burtaniya, Faransa da sauran wasu kasashen Tarrayar Turai. Don haka wannan kwance da kasar Amurka zai taimaka mana kwarai da gaske ta fuskar tsaro musamman ta kan samun bayanan wadanda za su shigo kasar mu, da wadanda ya kamata mu sakawa idanu, wanda kuma haka din ya rigaya ya fara tasiri."

Su ma dai mutanen biyu wadanda suka hada da Khalid Mohammed Salih Al-Dhuby mai shekaru 38, da kuma Mahmmoud Omar Mohmmed Bin Atef mai shekaru 36, sun nuna godiyarsu ga gwamnatin Ghana suna masu

"Mu ba 'ya'yan kowace kungiyar 'yan ta’adda bane misali Al-Qaida da suransu, kuma muna so mu zauna a kasar Ghana acikin kwanciyar hankali da lumana."

Sai dai Docta Kwasi Aning wani masani akan harkokin tsaro ya bayyana shakkunsa yana mai kan wadannan bayannai da shugaban da ma wadanda aka baiwa mafakar suka yi.

Barack Obama in Ghana Afrika

"Dabaru da yanayin da 'yan ta’adda ke amfani da shi wajen horar da jami’ansu tare kuma da sauya mu su tunani, na nufin cewar wadan nan mutane kwararru ne akan barar da tunanin jama’a. A bisa wannan dalili ina cikin matukar kaduwa, kuma abin ban takaici shi ne ba su damar yin bayanai a kafafun yada labarun kasar domin tabbatar wa al’ummar kasar nan miliyan 24 cewar ba su da wata barazana ga tsaron kasa."

Sai dai kawo yanzu ana ci gaba da zazzafan muhawara a duk fadin kasar a game da wannan batu, tare da nuna rashin gamsuwa da wannan matakin da gwamnati ta dauka. A dayan hannu kuma wata kungiyar farar hulla mai zaman kanta ta kasar Amurka, da ake kira Africa Center for International Law and Accountability (ACILA), ta shawarci majalisar dokokin kasar Ghana, da ta yi kwaskwarima akan dokar da ta baiwa bangaren zartaswar majalisar damar yanke wannan hukuncin ba tareda sanin jama’ar kasa ba.

Sauti da bidiyo akan labarin