1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Martanin dokar shafukan sada zumunta a Najeriya

Suleiman BabayoDecember 4, 2015

Kungiyar kare hakin jama’a ta Amnesty International ta soki yunkurin kafa dokar kula da shafukan sada zumunta.

https://p.dw.com/p/1HHXa
Africa on the Move Smart taxis
Hoto: DW

Akwai daurin shekaru biyu ga duk wanda aka samu da laifin buga bayanai na karya ko korafi ya sanya mayar da martani daga masu amfani da shafuka da ‘yan jaridu a kasar.

Kwanaki biyu a jere ‘yan majalisar datawa ta Najeriya suka dauka suna muhawara a kan wannan batu da ake kalon na da sarkakiiyar gaske a Najeriya, inda suka nuna damuwa a kan abin da suka kira wuce iyaka da ake yi a shafukan sada zumunta da bayanai da babu tabbas.

Symbolbild Frankreich Paris Anschläge Social Media
Hoto: Getty Images/AFP/L. Venance

Kokari na sanya takunkumi ga masu amfani da shafuka sada zumunta a Najeriyar wadanda suka yi fice da ma zama hanyar da milyoyin matasa ke samun bayyana ra'ayoyinsu wani lokaci a yanayi na huce haushin abubuwan da ke faruwa ya sanya murtani a kasar.

Dokar ba ta tsaya a shafukan sada zumunta kawai ba ta kai ga cusa jaridun da aka san cewa suna da ka'idoji da dokokin aiki a cikin wadanda za su iya fuskantar fushin hukuma na daurin shekaru biyu a gidan kaso. ‘Yan jarida na cikin masu sukar wannan lamari. Mallam Auwali Sauid Mu'azu editan jaridar Daily Stream da ke Abuja, wanda ya soki matakin. Sanata Bala In Na'Allah shi ne wanda ya kawo bukatar samar da doka.

DW - Africa on the move
Hoto: DW

Duk da wannan yunkuri da alamun tashen da shafukan sada zumunta ke yi a Najeriya zai ci gaba da karuwa a kasar, musamman a yanayin na dangantaka tsakanin masu mulki da wadanda ake jagoranta.