Martanin Amirka game da Kama madugun ′Yan adawan Uganda | Labarai | DW | 28.04.2011
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Martanin Amirka game da Kama madugun 'Yan adawan Uganda

Bayan tsafke shugaban 'yan adawan Uganda Kizza Besigye karo na huɗu cikiun wata guda da jami'an tsaro suka yi, Amirka ta fito fili ta nuna rashin jin daɗinta game da tauye masa hakkin gudanar da zanga-zanga da ake yi.

Ɗan adawan Uganda Dr.Kizza Besigye bayan an ji masa rauni a farkon Afirilu.

Ɗan adawan Uganda Dr.Kizza Besigye bayan an ji masa rauni a farkon Afirilu.

Ƙasar Amirka ta bayyana damuwa game da musguna wa madagun 'yan adawan Uganda Kizza Besigye da ɓangaren gwamnati ke yi. Wannan ya biyo bayan kama shi Besigye da jami'an tsaro suka yi karo na hudu cikin wata guda bisa zarginsa da yunƙurin shirya zanga-zanga ba tare da izini ba. Muƙaddashin sakataren harkokin wajen Amirka da ke kula da al'amuran Afirka wato Johnnie carson, ya ce ya tattauna da hukumomin kampala kan abin da ya kira cin zarafin Besigye da ake yi.

Waɗanda suka shaidar da kama shi madagun 'yan adawan na Uganda a ranar alhamis suka ce jami'an tsaro sun yi amfani da borkono mai sa hawaye tare da ragargaza madubin motar da ya ke ciki domin tsamo shi. Dama dai an harbe shi a hannu tun lokacin da ya halarcin zanga-zangar yin Allah wadai da tsadar rayuwa a farkon wannan wata na afrilu.

Gwamantin Yuweri Museveni ta ce ba za ta amince da duk wani nau'i na zanga-zanga ba. Yayin da shi Kuma Kizza Besigya mai shekaru 54 da haihuwa, ya sha alwashin gudanar da bore domin yin tir da abin da ya danganta da sakancin gwamnati na gaza ɗaukan matakan magance tsadar rayuwa da al'uma ke fiskanta.

Mawallafi: Mouhamadou Awal
Edita: Umaru Aliyu