Martanin AI kan hukuncin kisa ga sojojin Najeriya | Siyasa | DW | 06.10.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Martanin AI kan hukuncin kisa ga sojojin Najeriya

A wata alama ta kara nuna alamar yamutsewar lamura ga shugabannin Tarrayar Najeriyar da suka yanke hukuncin kisa kan wasu sojan kasar, kungiyar Amnesty International ta yi suka ga wannan hukunci.

A wani abun dake kara nuna alamar yamutsewar lamura ga masu mulkin Tarrayar Najeriyar da suka kai ga yanke hukuncin kisa bisa wasu sojan kasar dake yaki da ta'addanci, kungiyar Amnesty International tabi sahu wajen karin matsin lambar adawa da kisan dake dada girma ciki da wajen kasar a halin yanzu.

Kama daga kungiyoyin kare farar hula ya zuwa ga malaman addinai dama sauran masu fada a ji dai sannu a hankali tana dada fuskantar karin matsin lamba ga gwamnatin Tarrayar Najeriyar da makonni kusan uku ta yanke hukunci na kisa a bisa wasu sojan kasar 12 da ta zarga da tawaye a cikin yakin ta'addancin kasar dake ci ganga ganga.

To sai dai na baya baya cikin matsin dai na zaman kungiyar Amnesty International mai cibiya a Birnin London da kuma tabi sahu wajen nuna adawarta bisa hukuncin da ga dukkan alamu ya tada hankali cikin kasar kuma ke zaman na farko a lokaci mai nisa. Amnesty da a baya ta sha suka ga aiyyukan take hakin fararhula a cikin yakin dai, ta karkato da nufin kare sojan da a cewarta duk wani kokari na kisansu ke zaman karatun ganganci ne maras tushe.

Jami'a ta kungiyar, Susannah Flood, tace duk da kasancewar kungiyar bata kammla bin diddigin shari'ar sojojin da aka gudanar a cikin sirri ba, ba za ta amince da kokarin mahukuntan kasar na tabbatar da hukuncin da wata kotun sojan kasar ta kai ga yankewa makonni uku a kasar ba. Ko bayan 12 dai yanzu haka gwamnatin ta sake kaddamar da irin wannan shari'ar sirri kan wasu jerin 97 da suka hada da manyan jami'ai da ma kananansu da dama.

Amnesty International Symbolbild

AI ta soki Najeriya kan hukuncin kisa

Babban buri dai daga dukkan alamu, na zaman kokarin tauna tsakuwa don aya taji tsoro ga sojan da sannu a hankali ke nuna alamun tawaye bisa umani a matakai daban daban na yakin dake tafiyar hawainiya cikin kasar.

To sai dai kuma a fadar Dr. Sadiq Abba dake sharhi a bisa harkokin tsaro da siyasa, kuskure ne babba tunanin fara hukunci bisa sojan da har yanzu suke fafutukar neman nasara a cikin yakin dake zaman irinsa na farko a garesu.

"Wannan babban kuskure ne kuma zai kawo wa sojojin Najeriya illa a cikin yakin da suke da Boko Haram. Wanda aka kashe din nan na da abokai a cikin sojan nan, suna da wadanda suka samu horo tare. In an kashe su zai kashe musu kwarin gwiwa a cikin yakin da suke. Duk wanda ya dau wannan mataki to bai yi la'akari da abun dake faruwa a cikin Najeriya ba”

Gurguwar dabara ko kuma kokari na tabbatar da gyara a cikin yakin dai, daga dukkan alamu matsin na su Amnesty na kara bakanta ran yan mulkin na Abuja dake masa kallon kokari na yamutsa lamura, maimakon tabbatar da kawo gyara da ma kila kare yakin a cikin gaggawa. Abun da kuma a cewar Labaran Maku dake zaman ministan yada labaran kasar, kuma kakaki na gwamnati ba zata sabu ba, wai bindiga cikin tsakar ruwa.

“Wannan kungiyar ta Amnesty international ina ganin abun da suke so shine a juya hankalin al'ummar Najeriya kan sojoji, ko kuma akawo fitina cikin soja. Ko a hada kan kudu da arewacin kasar cikin fada. Ana son dai kawai a girgiza kasar nan a lalata mata tafiya, mu kuma muna da imani ba wani bane zai koya mana daga waje. Mun san hakkinmu ga al'ummarmu, sojojinmu sun san hakkinsu ga al'ummarsu. Muna roko in basu da wani taimako to su kyale mu ci gaba da yakin da zai kawo zaman lafiya cikin kasar nan”

Nigeria Präsident Goodluck Ebele Jonathan

Shugaban Najeriya, Goodluck Ebele Jonathan

Kokari na gyaran kasa ko kuma neman fasawa, kowa ya kai ga asara, dai ikirarin tafiya dai-dai a bangaren mahukuntan dai na zuwa ne a lokacin da take dada bulla Najeriyar na zaman daya daga kurar baya ga batu na tabbatar da mulki na- gari a daukacin nahiyar Afirka.

Rahoton cibiyar Mo Ibrahim mai bin diddigin mulki na-gari dai ta ambato kasar can baya a mataki na 37 a cikin 52 na kasashe na nahiyarAfirka wajen iya mulkin al'umma, haka kuma na zaman ta 30 a nahiyar ga kokarin bin doka.

Sauti da bidiyo akan labarin