Martani kan soke haramcin shiga Amirka | Siyasa | DW | 22.01.2021
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Martani kan soke haramcin shiga Amirka

Jim kadan bayan rantsuwar kama ragamar mulki, sabon shugaban Amirka Joe Biden ya soke haramcin shiga kasar da Trump ya dora a kan baki daga kasashe 10 da Musulmi ke da rinjaye.

	USA | Washington | Inauguration | Joe Biden im Oval Office

Joe Biden ya sanya hannu kan soke wasu matakai da Donald Trump ya dauka

Tuni dai al'ummomin wadannan kasashe suka fara bayyana mabanbamtan ra'ayoyi dangane da matakin na sabon shugaban kasar Amirkan Joe Biden. Ko shakka babu wannan matakin ya faranta ran al'ummar Musulmi a fadin duniya, abin da suke wa kallon fatali da mummunar akidar nuna wariya da tsohon shugaban kasar Amirkan Donald Trump ya yi kokarin sanya wa ta karfi da yaji kan dubun-dubatan Musulmi, ba don komai ba sai don kawai su Musulmi ne.

US Wahl 2020 Donald Trump

Wasu dokoki da matakan tsohon shugaban Amirkan Donald Trump sun zama tarihi

Wani dan kasar Yemen da yaki ya daidaita kasarsa wanda kuma ya samu gurbin karin karatu a Amirkan amma waccan dokar ta hanashi zuwa, ya yi godiya ga mai duka kan soke dokar da Biden ya yi. Ita ma wata mata mai sana'ar kwalliyar mata 'yar kasar Iran, Rahmaoot Hindary ta nuna farin cikinta da wanna matakin da ta ce zai yi matukar taimakamata wajen inganta sana'arta.

Karin Bayani: Martani kan kutsen magoya bayan Trump

To sai dai a hannu guda, kamar yadda Sirag Mustapha wani marubuci ke fadi, Amirka ce ya kamata ta yi murna da huldar da take da kasashen Musulmi lafiya, inda ya ce Amirkan na wasa ne kawai da hankulan kasashen Musulmi ta hanyar sanya su zaton cewa suke amfana da ziyara ko kulla hulda da kasashensu ke yi da ita bayan kuwa a zahiri ba don irin kudin da kasashen Musulmin ke zubawa a kasar Amirkan ba da tuni  ta durkushe. A watan Maris na shekarar 2017 ne gwamnatin toshon shugaban Amirkan Donald Trump ta sanar da haramtawa 'yan gudun hijira daga kasashen Musulmi 10 da kuma Koriya ta Arewa shiga kasar.

 

Sauti da bidiyo akan labarin