Martani kan kare makarantun Najeriya | Siyasa | DW | 07.11.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Martani kan kare makarantun Najeriya

A Najeriya kwarru a harkar ilimin boko da kare cin zarafin mata sun mayar da martani kan shirin samar da tsaro a makarantun sakandire na kasar.

Kadammar da wannan shirin da gwamnatin Najeriyar ta yi inda ta fara da sauyawa dalibai 2400 daga jihohi uku na Adamawa, da Borno da kuma Yobe da ke arewacin Najeriyar makarantun zuwa wasu jihohin da za su samu sukunin ci gaba da karatunsu, na zama matakin farko a aikace na aiwatar da shirin wanda tun a watan Mayun da ya gabata lokacin da Najeriya ta karbi bakuncin taron koli na tattalin arziki.

Najeriya da wasu kasashen duniya da suka yi taron dangi don kyautata tsaro a makarantun sakandiren biyo bayan kai hare-hare a makarantun da ma sace ‘yan matan sakandire na garin Chibok. Zaben makarantun 30 da za'a fara aiwatar da shirin a Najeriya ya sanya tambayar tasirin da wannan yunkuri xai yi da aka dade ana jiran faruwarsa? Malam Ahmed Tijjani Lawal shi ne sakataren gudarawa na kungiyar tsaffin dalibai na kwalejin gwamnatin tarayya.

"To in za'a samu tsaron yana da kyau to amma ai sai an bi tarihi in an duba, in ka kula a can baya ai malamai su ne ma ke samar da tsaron a kowane lokaci suna tare da dalibai. Mu bisa wannan ma muka ba da shawarar a rufe makarantun nan sai tsaro ya inganta a dawo da daliban."

To sai dai ministar kula da harkokin kudi ta Najeriya Dr Ngozi Okonjo Iweala ta bayyana cewa an yi kyakyawan tsari domin samar da tsaro a makarantun shi yasa ma aka fara zaben makarantun da za'a aiwatar da wannan shiri. Sai dai ga Malam Shehu Usman Abubakar wani tsohon Malamin makaranta na ganin fa akwai gyara.

Sauti da bidiyo akan labarin