Martani kan gallazawa wadanda ake zargi da ta′addanci | Labarai | DW | 12.12.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Martani kan gallazawa wadanda ake zargi da ta'addanci

Shugaban hukumar leken asiri ta Amirka ya mayar da martani kan gallazawa fursunoni da ake zargi da aikata ta'addanci

CIA Direktor - John Brennan

John Brennan shugaban hukumar CIA

Shugaban hukumar leken asirin kasar Amirka ta CIA, ya kare matakin da jami'an hukumar suka dauka na mafani da wasu hanyoyin gallazawa, domin tatsan bayanai daga wadanda ake zargi da ayyukan ta'addanci bayan hare-haren ranar 11 ga watan Satumban shekara ta 2001 a kan kasar ta Amirka.

John Brennan ya yi kalaman sakamakon sakin rahoton majalisar dattawa, wanda ya nuna cewa hanyoyin gallazawar basu da wani inganci.

Brennan yana cikin manyan jami'an hukumar ta CIA a shekara ta 2002 lokaci da aka tsara shirin.

Mawallafi: Suleiman Babayo
Edita: Umaru Aliyu