Martani kan faduwar jirgin sama a Ukraine | Labarai | DW | 18.07.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Martani kan faduwar jirgin sama a Ukraine

Amirka ta ce an yi amfani ne da makami mai linzami wajen harbo jirgin saman Malesiya wanda ya fadi a ranar Alhamis din da ta gabata a gabashin Ukraine.

Shugaban Amirka Barack Obama ya ce kasarsa na da tabbacin cewar an yi amfani ne da makami mai linzami wajen harbo jirgin saman na Malesiya jiya Alhamis a yankin da 'yan awaren Ukraine da ke goyon bayan Rasha ke iko da shi.

Obama ya ce ya zuwa yanzu ba su san takamaiman wanda ya sa aka harbo jirgin ba da ma dalilin yin hakan, inda a hannu guda ya shawarci Rasha da ta tashi tsaye wajen ganin an kawo karshen rikicin da yakin ke fama da shi.

Wadannan kalamai na Obama dai na zuwa ne dai dai lokacin da masu sanya idanu na kungiyar tsaro da hadin kan Turai ta OSCE ta yi korafin gaza samun damar kai wa ga inda jirgin ya fadi domin gudanar da bincike.

Mawallafi: Ahmed Salisu
Edita: Suleiman Babayo