1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Najeriya: Sauke kwamandan sojoji

April 1, 2020

A Najeriya masana na tofa albarkacin bakinsu kan matakin da rundunar sojojin Najeriya ta dauka na sanar da cire Manjo Janar Olusegun Adeniyi kwamandan rundunar yaki da Boko Haram da aka fi sani da Operation Lafiya Dole.

https://p.dw.com/p/3aK9U
Symbolbild | Soldaten | Kamerun
Sojojin Najeriya a fagen dagaHoto: Getty Images/AFP/A. Huguet

Rundunar sojojin Najeriyar dai ta cire Manjo Janar Olusegun Adeniyi ne bayan da ya aike da wani faifen bidiyo ga shelkwatarsu kan yadda su ke fama da karancin kayan aiki. Matakin na cikin wata sanarwa da aka rabawa manema labarai. Ana dai alakanta cire Manjo Janar Adeniyi da wannan faifayin bidiyon da ya dauka a filin daga inda ya ke nuna yadda su ke da karancin kayayyakin aiki da yadda motocinsu suka tsaya a daidai lokacin da su ke gwabza yaki da Boko Haram. Kawamndan Manjo Janar Adeniyi ya tabbatar a wannan faifayin na bidiyo cewa, sojojin  na filin daga da kwamandojinsu kuma ba wanda ya gudu kamar yadda ake zargi.

Sauyin abu ne mai kyau

Faifen bidiyon da aka nufi aikewa da sako ga babban hafsan sojojin kasar domin sanin halin da rundunar yakin ke ciki dai, ba a san yadda aka yi ya fita har aka yi ta yada shi ba. A cewar wani tsohon soja Kolomi Dala sauyi kwamandan na da fa'ida, saboda ko ba komai sabon kwamandan zai zo da sababbin dabaru kuma zai dauki darasi daga kurakrai da ake ganin wanda aka cire ya yi.

DW Still Boko Haram kill 65 people at funeral in Nigeria
Hare-haren Boko Haram na kara ta'azzara

Bujatar sauya shugabannin sojoji

A cikin shekaru 2 biyu kacal dai an samu sauyin kwamnadojin wannan runduna guda biyar abinda ya sa masu fashin baki kan al'amuran tsaro irinsu Malam Tijjani Usman ke ganin yawan canjin ba abu mai kyau ba ne. A nasu bangaren masu fafutukar wanzar da zaman lafiya na da ra'axyin cewa matsaloli da koma baya da ake samu na kokarin wanzar da zaman lafiyar, na bukatar samun sauyi ne a daukacin shugabancin tsaro na kasar baki daya ciki kuwa har da dukkanin manyan hafoshin tsaro na kasar. Sai dai shugaban Najeriya ya sa kafa ya shure dukkanin wani hankoro da aka yi na neman sauya manyan hafsoshin tsaron, bayan da su ka kwashe sama da shekaru da kuma karuwar tabrbarewar tsaro a kusan dukkanin yankunan Arewacin kasar.