Martani kan ƙuri′ar majalisa | Siyasa | DW | 11.11.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Martani kan ƙuri'ar majalisa

A Jamhuriyar Nijar bayan da gwamnati ta yi nasarar ketara siradin auna matsayinta a majalisar dokoki wasu 'yan kasar sun soma tofa albarkacin bakinsu

default

'Yan kasar Jamhuriyar Nijar na bayyana ra'ayi kan nasarar da gwamnatin Firaraminista Briji Rafini ta samu a majalisar da kuma abin da suke jira daga gwamnati.

'Yan majalisar dokoki 70 daga cikin 113 da majalisar ta kunsa
suka ba da goyon baya ga gwamnatin ta Firamnista Briji Rafini, bayan wata zazzafar mahawarar da ta gudana a majalisar dokokin kasar a karshen makon da ya gabata. Kuma tuni batun wannan mahawara ta majalisar ya zama a sahun gaban duk wasu hirarraki da ke gudana a wuraran taruwar jama'a musamman dangane da yadda sakamakon ya bayar da kuma tasirin da zai yi wajen kawo karshen cece-kucen siyasar da ya dabaibaye kasar, tun bayan yunkurin shugaban kasa Mohamadou Issoufou na kafa gwamnatin hadin kan kasa. Jamiy'yar PND Awaiwaya ta bakin shugabanta Malam Suma'ila Amadu jinjina wa gwamnatin ta yi tare kuma da yin hannunka mai sanda.

Daga nasa bangare Malam Sule Maje wani dan jarida mai sharhi a kan al'amurran siyasar kasar ta Nijar cewa ya yi sakamakon zaben da majalissar ta yi na cike da darasi na siyasa.

To sai dai duk da nasarar da gwmanatin ta samu wasu na dora ayar tambaya dangane da sahihancin sakamakon zaben; Kungiyar farar hula ta MOJEN na daga cikin masu irin wanann ra'ayi kamar dai yadda Malam Habila Rabi'u mataimakin shugaban wanann kungiya ta Mojen ya bayyana.


Martanin 'yan adawa

A cikin wata sanarwa da ya fitar a yau sabon kawancan gambizar wasu jam'iyyun adawa da kungiyoyin farar hula na Nijar mai suna FDJD cewa ya yi sakamakon da gwamnatin ta samu bai da wani tasiri domin suna zargin akwai lauje cikin nadi.

Ya zuwa yanzu dai jama'a sun zuba ido su ga tasirin da wanann sakamakon na gagarumin rinjaye da gwamnati ta samu a majalisar dokokin kasar kawo karshen cecekucen siyasar da ya biyo bayan kafa gwmanatin hadin kan yan kasa a kasar ta Jamhuriyar Nijar.

Mawallafi: Gazali Abdou Tasawa
Edita: Suleiman Babayo

Sauti da bidiyo akan labarin