1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Martani ga mutuwar marigayi shugaba 'Yar'adua

May 6, 2010

Shugabannin ƙasashen duniya sun bayyana maigayi 'Yar'adua a matsayin shugaba na - gari.

https://p.dw.com/p/NG0O
Hoto: AP

Shugabannin Duniya daban daban na ci gaba da miƙa saƙonnin ta'aziyyar su ga tsohon shugaban Nijeriya Marigayi Malam Umaru Musa 'Yar'adua, wanda Allah ya yiwa cikawa a yammacin jiya Laraba, bayan da ya yi fama da rashin lafiya. A saƙon ta'aziyyar sa babban sakataren Majalisar Ɗinkin Duniya Ban Ki Moon ya ce daga cikin kyawawan abubuwan da za'a tuna da 'Yar'adua sun haɗa da ƙoƙarin sa na kawo zaman lafiya a yankin Neija Delta - mai arziƙin man fetur dake ƙasar da ƙudurin sa na samar da kyakkyawan shugabanci da kuma wanzar da tsarin dimoƙraɗiyya game da samar da sauye sauye a tsarin zaɓukan ƙasar. Shima shugaban Amirka Barak Obama cewa ya yi marigayi shugaba 'Yar' adua ya taka rawar gani wajen samar da zaman lafiya a tsakanin ƙasashen da ke da iyaka da Nijeriya. Shugaba Jacob Zuma na ƙasar Afrika ta kudu kuwa bayyana kyakkyawan fatan sa ya yi na cewar, nahiyar Afirka za ta yi anfani da kyakkyawar manufar marigayi 'Yar'adua wajen samar da ci gaba a nahiyar Afirka. Idan dai ba'a manta ba tun lokacin jawabin kama aikin da marigayi 'Yar'adua ya yi ne ya bayyana ƙudurin samar da zaman lafiya a yankin na Neija Delta:

"Rikicin yankin Neija Delta na buƙatar kulawarmu cikin hanzari. Kawo ƙarshen sa abune mai muhimmancin gaske ga ƙasar mu. Zan yi amfani da duk wata damar da nake da ita - tare da taimakon ku wajen warware wannan rikicin, ta hanyar tabbatar da adalci da daidaito da kuma haɗin kai."

Mawallafi : Saleh Umar Saleh

Edita : Muhammad Nasir Awal