1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Marshal Al-Sisi ya lashe zaben shugaban kasa a Masar

May 30, 2014

Bayan da hukumar zaben Masar ta bayyana sakamakon zaben shugaban kasar da tace, Fil Mashal Al Sisi ne ya lashe da gagarumin rinjaye, yan kasar da ma kasashen Larabawa na ci gaba da yin martini kan zaben.

https://p.dw.com/p/1C9Un
Kombobild Hamdien Sabahi und Abdel Fatah al-Sisi
Hoto: picture-alliance/dpa

Bayan da hukumar zaben Masar ta bayyana sakamakon farko na zaben shugaban kasar da tace, Fil Mashal Al Sisi ne ke kan gaba da gagarumin rinjaye, yan kasar da ma kasashen Larabawa na ci gaba da yin martini kan zaben.

Farawa da dan takarar da ya sha kaye a zaben, Hamdain Sabbahi, wanda bayan da ya ce ya rungumi kaddara duk da magudin da aka tafka a zaben, ya kara da bayyana rashin aniyar karbar wani duk makami da za a yi tayin bashi a gwamnatin da ke tafe.

'Ina mutunta zabin da 'yan kasa suka yi. Na amince da kayen da aka yi mini. Ko da yake ba ta yadda za a yi mu amince da alkaluman da hukumar zabe ta bayar, domin alkalan na boge ne."

Kamar dai yadda dokakin hukumar zaben suka tanada, ba wanda zai yi suka, ko kara kan sakamakon da za ta bayar,s awa'un dan takara ne ko mai kada kuri'a. Sabanin ikirarin yin aringizon kuri'u da Sabbahin yayi, ita kuwa kungiyar kasashen Larabawa, a ta bakin shugabar kwamatin sa ido a zaben na kungiyar, Haifa Abu Gazalah, cewa tayi an yi zaben cikin gaskiya da bin tsarin doka;

"Kungiyar kasashen Larabawa tana ba da tabbacin cewa, bayan da ta bi diddigin yadda zaben ya gudana, 'yan kura-kuren da aka samu a zaben ba su kai yadda za su yi lahani ga sahihancin sakamakon zaben ba."

Suma talakawan na Masar ba a bar su a baya ba wajen tofa albarkacin bakinsu kan zaben, ra'ayoyin dake nuna irin zaman yan marinan da ke tsakanin 'yan kasar.

"A ganina wannan zabe yayi matukar kyau. Wadanda kuma suka kaurace masa don kansu. Ba za dai su hana jirginmu tashi ba."

Itama wannan matar ga abin da take cewa:

"Nayi matukar murna da zaben Al Sisi da aka yi.Yanzu zai sami karfin guiwar tunkarar ta'addancin dake addabarmu da kuma magance matsalolin da suka zamo mana karfan kafa."

Shi kuwa Ahmad Shahada, kakakin jam'iyar adawa ta Al'asala mai ra'ayin Islama cewa yake:

"Dole ne mu fito mu yi dandazo kan tituna don ganin bayan wadannan yan banga dake neman yin garkuwa da 'yan Masar. Ba zamu sarara ba har sai munga irin gwamnatin Mubarak bata dawo kan mulkin kasar nan ba."

Präsidentschaftswahlen in Ägypten 28. 05. 2014
Hoto: Mohammed Mahjoub/AFP/Getty Images

Shi kuwa Tariq Awad, shugaban tsangayar kimiyar siyasa a jami'ar Hilwan nuna mahimmancin sasanta tsakanin illahirin yan kasar yayi:

"Akwatin zabe, da shi kansa zabenkadan ne daga cikin hanyoyin samar da halarcin shugabanci a tsarin dimokiradiyya, amma babban halaccin shugabanci shine samarwa yan kasa da yanci da walwala,da kuma kyautatawar rayuwa gami da samun daidaito wajen rabon arzikin kasa."

Mawallafi: Mahmud yaya Azare
Edita: Umaru Aliyu