Maroko: Ana zaben ′yan majalisar wakilai | Labarai | DW | 07.10.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Maroko: Ana zaben 'yan majalisar wakilai

Jam'iyyu 30 ne ke fafatawa, kuma akwai zazzafar gasa tsakanin masu ra,ayin Islama da 'yan gurguzu.

A wannan Juma'arce al'ummar kasar Maroko ke gudanar da zaben sabbin 'yan majalisa, shekaru biyar bayan da gwamnati mai ra'ayin Islama ta dare karagar mulkin wannan kasa bayan juyin juya halin da ya yi awon gaba da gwamnatocin kasashen larabawa da dama.

 Duk da cewar jam'iyyu 30 ne ke fafatawa, Jam'iyyar PJD mai ra'ayin Islama na kalubalantar manufofin ta adawa ta PAM, wadda ke muradin sake warware tsarin mulkin kasar da ke tafarkin Islama.

Sai dai duk da haka, Sarki Mohammed na shida zai ci gaba da rike madafan iko, a wannan masarautar da kemulkin kasar ta yankin arewacin Afirka na tsawon shekaru 350.

Rahotanni na nuni da cewar, mutane basu fito don kada kuri'unsu ba, inda akasari ke jira sai bayan sallar juma'a.

Domin saukakawa mutanen da basu iya karatu ba, wadanda sune kashi daya daga cikin ukun al'umma, an sanya alamun wasu hotuna kamar Rakumi ko Mota, da zasu fayyace kowane daga cikin jam'iyyu 30 dake takara.