1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kasashe uku na sun sha alwashin sauyi a EU

Yusuf BalaJune 27, 2016

Shugabannin wadannan kasashe sun ce babu wata tattaunawa a hukumance ko akasin haka sai an ji daga mahukuntan na Birtaniya.

https://p.dw.com/p/1JEg1
Deutschland Berlin PK Merkel Renzi und Hollande
Hollande da Merkel da RenziHoto: Reuters/H. Hanschke

Shugabanni daga kasashen Faransa da Italiya da Jamus sun bayyana cewa za su dauki sabbin matakai na sake kullewa tsakanin juna inda za su ci gaba da ayyukan ci gaba tsakanin kasashe 27 na kungiyar EU bayan da Birtaniya ta dauki mataki na raba gari da kungiyar.
Bayanin hakan ya fito ne bayan da shugaba Merkel ta Jamus ta karbi bakuncin wadannan shugabanni na manyan kasashe uku da ke cikin wannan kungiya ta EU a birnin Berlin. Shugaba Merkel da Francois Hollande da Firaminista Matteo Renzi sun dai ce babu wata tattaunawa a hukumance ko ba a hukumance ba kan batun ficewar ta Birtaniya har sai an turo da bukatar neman barin wannan kungiya daga mahukuntan na Birtaniya.