1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaJamus

Manyan kasashe sun gargadi Sudan

January 5, 2022

Bayan murabus da firaminista ya yi da ma zangar-zangar adawa da mulkin soja a Sudan, kasashe sun ce ba sa goyon nadin wani da ya ci karo da ra'ayin 'yan kasar.

https://p.dw.com/p/459Z8
Sudan Khartoum | Protesten gegen den Militärputsch
Hoto: AFP/Getty Images

Kasashen Amirka da Birtaniya da Norway da ma Tarayyar Turai, sun gargadi jagororin soja a Sudan cewa ba za su goyi bayan nada sabon firaministan ba, sai har idan 'yan kasar ne suka aminta da shi.

Manyan kasashen na duniya, sun yi barazanar janye duk wani tallafin da suke bai wa Sudan, idan har sojojin suka yi gaban kansu wajen nada wani nasu a matsayin sabon firamnistan.

Wannan na zuwa ne sakamakon boren da 'yan Sudan ke ci gaba da yi na adawa da mulkin soja, bayan murabus da tsohon firaminista Abdallah Hamdok ya yi a ranar Lahadin da ta gabata.