Manyan kasashe sun bijire wa shirin Amirka | Labarai | DW | 20.12.2018
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Manyan kasashe sun bijire wa shirin Amirka

Manyan kasashen Turai da ke kawance da Amirka a yaki da kungiyar IS, sun nuna damuwa kan matakin na Shugaba Donald Trump na janye dakaru daga Siriya.

Shugaba Racep Tayyip Erdogan na kasar Turkiyya da takwaransa na Iran Hassan Rouhani, sun yi alkawarin ci gaba da kokarinsu na dawo da zaman lafiya a Siriya.

Shugabannin biyu dai sun sanar da hakan ne bayan sanar da janye dakarunta sama da 2000 da Amirka ta ce za ta yi daga Siriyar, saboda abin da ya kira na nasarar karya lagon mayakan IS da aka yi a can.

Manyan kasashen Turai da suka hada da Birtaniya da Jamus da kuma Faransa da ke kawance da Amirka a yaki da kungiyar IS, sun nuna damuwarsu kan matakin na Shugaba Donald Trump.

Kasashen dai na ganin hakan ya zo ne a lokacin da kungiyar ke da sauran karfinta a yankuna da dama na Siriya.

Ko a makon jiya ma Shugaba Erdogan na Turkiyya, ya yi barazanar kaddamar da sabbin hare-hare kan mayakan Kurdawa wadanda ke samun goyon bayangwamnatin Amirka.