1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Manyan jami'an diplomasiya na ci gaba da tattaunawa da Iran

Mohammad Nasirun AwalApril 2, 2015

Ministan harkokin wajen Iran ya yi kyakkyawan fatan cimma yarjejeniya tsakanin kasarsa da kasashen da ke tattaunawa da ita kan shirinta na nukiliya.

https://p.dw.com/p/1F20C
Bildergalerie Iran Atomverhandlung Schweiz Lausanne
Hoto: Isna

A wannan Alhamis ministan harkokin wajen Iran Mohammad Javad Zarif ya ce yana da kyakkyawan fata nan ba da jimawa ba Iran da kasashe shida da suka shiga tattaunawa da ita kan shirinta na nukiliya za su fid da wata sanawar hadin guiwa idan an cimma wata yarjejeniya kan warware takaddamar.

"Sanarwar za ta kasance ta manema labaru wadda abokanmu za su yi aiki kai. Amma ba mu san yadda za ta kasance ba domin har yanzu ana bukatar tattaunawa tsakanin kasashen shida kuma har yanzu ba mu san batutuwan da suke shawartawa kai ba. Amma da yardar Allah za a ba da sanarwar hadin guiwa da ni da wakiliyar tarayyar Turai Federica Mogherini da ke wakiltar wannan gungu."

Manyan jami'an diplomasiya na kasashe masu kujerun dindindin a Kwamitin Sulhun Majalisar Dinkin Duniya hade da Jamus na ci gaba da tattaunawa da kasar ta Iran a Lausanne da ke kasar Switzerland a kokarin cimma masalaha game da shirin nukiliyar gwamnatin Teheran.