Manyan jami′ai ke tallafa wa Boko Haram a Najeriya. | Siyasa | DW | 29.08.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Manyan jami'ai ke tallafa wa Boko Haram a Najeriya.

Ali Modu Sheriff tsohon gwamnan jihar Borno da Laftanan Janar Azubuike Ihejirika tsohon hafsan hafsoshin soja, su ake zargi da tallafa wa Kungiyar nan ta Boko Haram a Najeriya.

A hira da tashar Telebijin ta Arise da ke zama reshen kamfanin da ke buga jaridar This Day a Najeriya, Dr. Stephen Davis dan kasar ta Australiya wanda ya kwashe watanni hudu yana tattaunawa da kungiyar Boko Haram a madadin gwamnatin Najeriya, ya ce tsohon gwamnan jihar Borno kuma sanata a yanzu Ali Modu Sheriff da kuma tsohon hafsan hafsoshin sojin Najeriya Laftanan Janar Azubuike Ihejirika ke tallafa wa kungiyar ta masu tayar da kayar baya a arewa maso gabashin Najeriya. Sai dai a cikin fushi mutanen biyu sun musanta wannan zargi suna masu cewa babu wata ribar da za su samu wajen tallafa wa Boko Haram.

A cikin hirar Dr. Davis ya ce mayakan Boko Haram suka shaida masa cewa akwai manyan 'yan siyasa da ke sama wa kungiyar kudade, saboda haka ya yi kira da'a kame mutanen.

Ya ce: "Abin da ya kamata a fara yi a Najeriya shi ne kame masu tallafa musu. Hakan zai rage fadan, kuma rundunar sojin Najeriya za ta samu damar murkushe Boko Haram. A fara kame tsohon gwamnan Borno Sheriff wanda ya kwashe shekaru yana ba su kudi. dan ya san za'a iya kama shi, ya sa ya canja sheka ya koma jam'iyyar PDP da fatan za ta ba shi kariya."

To sai dai a hira da tashar DW, Heinrich Bergstresser kwararren masanin siyasa da tsaro da kuma zamantakewar al'ummar Najeriya, ya ce zai yi wuya hankali ya dauki wannan maganar domin bai dace ba kuma rashin basira ne wani daga wata duniya ya zargi wannan mutanen ba tare da ya ba da wata kwakkwarar sheda ba.

Ya ce: "Hakika Ali Modu Sheriff ya taimaka wajen kirkiro kungiyar Boko Haram kafin ta rakide zuwa kungiyar 'yan ta'adda. Amma shi din ne ya fito da ita fili yayi amfani da ita don cimma muradunsa na siyasa. Daga bisani ya yi amfani da jami'an tsaron don murkushe ta. Amma daukar wannan yanzu a matsayin hujjar zarginsa da tallafa wa kungiyar a gani na bai dace ba."

A dangane da Laftanan Janar Azubuike Ihejirika kuwa, masanin na Najeriya cewa ya yi, ya ba da gudunmawa wajen sama wa rundunar Najeriya canja tsarin yaki da ta'addanci ya zuwa wata harkar kasuwanci ta yaki da Boko Haram. To sai dai abin bakin ciki ba wani mahaluki a cikin manyan hafsoshin kasar da ke da sha'awar ganin an samu nasarar yaki da ta'addanci saboda makudan kudaden da ake ware wa wannan sashe. Irin wannan matsalar na faruwa a ko ina cikin duniya saboda kudaden da ke cikin yaki da ta'adda.

Shi dai Dr. Stephen Davis ya ce idan aka kama mutanen biyu da sunan suna daure wa Boko Haram gindi, to kungiyar za ta yi rauni. To amma Heinrich Bergresser ya ce ai ba nan gizo ke saka ba.

Ya ce: "Ainihin masu tallafa wa kungiyar, mutane ne kuma sanannu a tsakanin gwamnati, sun hada har da wani tsohon gwamnan arewacin Najeriya, ban da Sheriff, su ya zama wajibi a gurfanar da su gaban kuliya. Amma gaskiya magana ita ce gwamnati ba ta da sha'awar tinkarar wannan matsala."

Kasancewa yanzu hankali ya karkata ga zaben 2015 a Najeriya, gwamnati ba ta ba wa rikicin Boko Haram muhimmanci. Watakila bayan zaben idan wannan gwamnati ta lashe za ta sake lale a matakan yaki da kungiyar.

Mawallafi: Muhammad Nasiru Awal
Edita: Yusuf Bala

Sauti da bidiyo akan labarin